Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Alin Kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza

Ali kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza a
dambatawar da suka yi da yammacin Talata a
gidan dambe na Aminu Goje da ke Alaba Rago
da ke jihar Legas.
Ali Kanin Bello dan damben Arewa ya yi nasarar
doke Shagon Reza Bunza dan wasan Guramada
a turmin farko da suka zare.
Wasa na biyu tsakanin Shagon Ummaru Mugu
Guramada da Autan Yahaya Kwantagora daga
Arewa tashi suka yi babu wanda ya je kasa.
Shikuwa Shagon Cindo Guramnada buge Autan
Sunusi dan Bunza daga Arewa ya yi a turmi na
uku.
Wasa na karshe tsakanin Shagon Ummaru
Guramada da Dan Hussaini daga Jamus turmi
uku suka yi babu kisa.
Alin Kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza Alin Kanin Bello ya buge Shagon Reza Bunza Reviewed by Mr Amanagurus on November 15, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.