Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Amurkawa na fama da jarabar shan miyagun kwayoyi

Shugaban kiwon lafiyar al'uma na Amurka ya yi
kira dauki matakin gaggawa domin magance
matsalar jarabar shan miyagun kwayoyi da
barasa.
Vivek Murthy ya ce shan miyagun kwayoyi da
barasa na daya daga cikin matsaloli mafiya
tsanani a wannan zamani.
A cikin wani rahoto na farko irinsa, Vivek Murthy,
ya ce shan miyagun kwayoyi na shafar muliyoyin
Amurkawa, da kuma janyo asara ta $50000m a
kowace shekara.
A cewarsa, duk da wannan matsalar, mutum
daya ne kacal cikin goma ke yin jinya.
Admiral Murthy ya jaddada cewa akwai bukatar a
sauya baki dayan yadda ake tunkarar lamarin,
yana mai cewa maimakon a rika daukar shan
miyagun kwayoyi a matsayin matsalar lalacewar
tarbiya, ya kamata a rika kallon lamarin a
matsayin wata mummunar cuta tamkar sankara
ko ciwon sukari.
Amurkawa na fama da jarabar shan miyagun kwayoyi Amurkawa na fama da jarabar shan miyagun kwayoyi Reviewed by Mr Amanagurus on November 17, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.