Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Brazil za ta karbi bakuncin Argentina

Tawagar kwallon kafa ta Argentina za ta ziyarci
Brazil domin buga wasan shiga gasar cin kofin
duniya a ranar Alhamis.
A wasan farko da kasashen biyu suka fafata a
gidan Argentina kunnen doki 1-1 da suka tashi.
Brazil wadda ke mataki na uku a jerin kasashen
da suke kan gaba a taka-leda a duniya ta hadu
da Argentina wadda ke matsayi na daya a
jadawalin Fifa, sau 102.
Brazil ta ci wasanni 39, ita kuwa Argentina ta
samu nasara a karawa 37, sannan suka yi
canjaras a fafatawa 26.
Bayan da Kudancin Amurka suka yi wasanni 10,
Brazil ce a matsayi na daya sai Uruguay sannan
Equador, Argentina tana mataki na shida.
Ga sauran wasannin da aka za a yi:
Colombia vs Chile
Uruguay vs Ecuador
Paraguay vs Peru
Venezuela vs Bolivia
Brazil za ta karbi bakuncin Argentina Brazil za ta karbi bakuncin Argentina Reviewed by Mr Amanagurus on November 09, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.