Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Faransa: An cika shekara guda da kai hare hare

Ana gab da fara bukukuwar cika shekara guda
da kai harin da ya hallaka sama da mutane dari
a birnin Paris.
Shugaba Francois Hollande da magajin birnin
Paris ne za su jagorance daga tutar tunawa da
wadanda suka hallaka a wurare shida da akai kai
hare-hare mafi muni da kasar ta fuskanta cikin
shekaru masu yawa.
Tun da farko Firaiministan Faransa Manuel Valls
ya shaidawa majiyarmu cewa mai yiwuwa a kara
tsawaita wa'adin dokar ta bacin da aka sanya a
kasar .
A halin yanzu an sake bude babban dakin kallon
Sinima na Bataclan inda masu kallo suka yi shiru
na minti daya don tunawa da mutane 89 da 'yan
bindiga suka kashe a cikin wurin.
'Yan uwa da iyalan mutanen da suka mutu ne
suka halarci gidan siniman.
Faransa: An cika shekara guda da kai hare hare Faransa: An cika shekara guda da kai hare hare Reviewed by Mr Amanagurus on November 13, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.