Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Harin bom ya halaka mutane 43 a Karachi

Jami'ai a Pakistan sun ce akalla mutane 43 ne
suka mutu sakamakon tashin bom a wani wurin
ibada na Musulmai sufaye, a arewacin birnin
Karachi.
Kafofin yada labarai na cikin kasar sun ce
mutane da dama ne suka jikkata a harin.
Harin ya auku ne yayin da rana ke fitowa, lokacin
da akalla mutane dari biyar suka taru a wurin
ibadar domin gudanar da al'amuransu.
Motocin daukan marasa lafiya sun shafe sa'o'i
kafin su isa wurin, amma daga baya, sun kwashe
wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
An kai harin ne watanni bayan an harbe Amjad
Sabri, wani fitaccen mawakin Sufanci a Karachi.
Harin bom ya halaka mutane 43 a Karachi Harin bom ya halaka mutane 43 a Karachi Reviewed by Mr Amanagurus on November 12, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.