Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Trump: Ba zan gurfanar da Hillary gaban kotu ba

Shugaban Amurka mai-jiran-gado Donald Trump
ci gaba da yin watsi da tsauraran alkawuran da
ya yi lokacin yakin neman zabe - inda a yanzu
ya yi watsi da batun gufanar da Hillary Clinton
gaban kotu kuma ya ce ba zai kafe kan ra'ayi
guda ba kan batun sauyin yanayi.
A cikin wata doguwar hira da jaridar New York
Times, Mr. Trump ya ce ba zai so ya bata wa
iyalin Clinton rai ba, yana mai cewa shi yana son
ya manta abin da ya wuce baya ne.
Da aka tambaye shi game da goyon bayan da ya
samu daga kungiyar Alt-right ta masu ra'ayin
rikau da masu zazzafan kishin fararen fata, Mr.
Trump ya ce ya yi tir da al'amarinsu kuma bai
san da zamasu ba.
Ya ce ba zai so ya ba kungiyar da ta kunshi
masu ra'ayin 'yan Nazi da masu tsananin kishin
farar fata da kuma masu kyamar Yahudawa
kwarin gwiwa ba.
Trump: Ba zan gurfanar da Hillary gaban kotu ba Trump: Ba zan gurfanar da Hillary gaban kotu ba Reviewed by Mr Amanagurus on November 22, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.