Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya
kare shirinsa na karbar mulki yayinda ake tsaka
da samun rashin jituwa a cikin tawagarsa.
Mista Trump, hamshakin mai hada-hadar gidaje
ne kuma sabon shiga ne a jam'yyar Republican
wanda ya yi nasarar ba-zata a kan Hillary
Clinton.
Tuni dai Trump ya maye gurbin gwamnan New
Jersey Chris Christies da zababben mataimaki
Mike Pence a matsayin shugaban kwamitin mika
mulki.
Kafafen yada labarai na Amurka sun ce an
tursasa wa manyan mambobin kwamitin mika
mulkin biyu, wandanda ke aiki kan tsaron barin
ayyukansu.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce
surikin shi da kuma Jared Kushner wani mai ba
shi shawara wanda yake da kusanci da shi suna
da hannu a sauyin.
Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa Trump ya ce babu matsala a cikin tawagarsa Reviewed by Mr Amanagurus on November 16, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.