A jiya ne shugaban kamfanin MTN wato Ferdinend Moolman ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dau tsatstsauran mataki akan manya kamfanonin sadarwa na zamani guda biyu wato WhatsApp da Facebook. Shugaban ya bayyana cewar WhatsApp da Viber sun kawo ci baya wa kamfanonin sadarwa na cikin gida inda yake ganin cewar suna wawushe dukiyar da ya kamata ace sune suke samu, a sabili da haka ya bukaci a dakatar da su kamar yadda hadaddiyar daular larabawa (UAE) suka yi. A bayyane yake cewar WhatsApp na bawa al ummah damar yin abubuwa da yawa, kama daga tura sakonni masu tsayi, tura hotuna, sauti, hoton video, manhajoji da sauran makamantansu wanda har ta kaiga zaka iya yin kira kyauta(free call) ba tare da an caje ka ko sisi ba. A yanzu haka baka da damar yin kiran WhatsApp ko na SnapChat a hadaddiyar daular larabawa (UAE) wanda bijerewa dokar ka iya jawo a kama mutum ko kuma a ci mutum tara. |
Kamfanin MTN Ya Bukaci A Dakatar Da Whatsapp Da Viber A Nigeria
Reviewed by Mr Amanagurus
on
December 07, 2016
Rating:
No comments: