Sufeta Janar na ‘Yan Sanda zai binciki wayar da ake zargin Gwamnan Rivers yayi da Ma’aikatan zabe
– An ji muryar Gwamnan Rivers, Nyesom Wike a wayar tarho yana kokarin murde zabe
– Haka kuma an ji Gwamnan yana cewa zai kashe Ma’aikatan INEC din idan ba su yi yarda yake so ba

Wani Gwamna ya shiga uku ya lalace
Gwamnan Jihar Rivers ya shiga cikin ha’u’la’i a halin yanzu, don kuwa Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Kasa ya saka bincike game da muryar da aka ji a wayar tarho na shi Gwamna Wike da yake yunkurin murde zabe.
An samu muryar wayar tarho da Gwamnan Jihar Rivers yayi da Jami’in Hukumar zabe na INEC. An ji Gwamnan da kan sa yana shan alwashin kashe daya daga cikin Jami’an zaben da aka turo Jihar daga Plateau.
Wani Gwamna ya shiga uku ya lalace
Jairdar Sahara Reporters ce dai ta fito da wannan sauti. An ji cewa Gwamnan yayi alkawarin kashe wani Jami’i da ya gagara da aka tur aiki daga Jihar Plateau. Gwamnan ya bada kudi domin a murde zaben Jan’iyyar PDP ta samu nasara.
Mataimakin Kwamishina na ‘Yan Sanda Don N. Awunah, ya bayyana cewa Sufeta-Janar, Ibrahim K. Idris ya sa ayi bincike game da lamarin. Hukumar ‘Yan Sanda na Kasar ta nada kwamitin da ke dauke da wani kwararre a harkar bincike. Za a gabatar da wannan aiki cikin wata guda, kuma a fitar da sakamako.
Wani Gwamna ya shiga uku ya lalace
Reviewed by Mr Amanagurus
on
December 18, 2016
Rating:
No comments: