Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Bukin rantsarda sabon shugaban Ghana ya kankama

Kasar Ghana ta shirya tsaf domin bukin rantsar
da Nana Akuffo Addo a zaman shugaban kasar
na 12 a tarihi kuma na 5 a jamhuriya ta hudu.
Da misalin karfe 10 na safiyar yau Assabar
agogon kasar ne za a rantsar da sabon shugaban
a yayin wani gagarumin biki a Accra babban
birnin kasar.
Hakan ya biyo bayan da Nana Akuffo Addo -
wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil'adama -
ya kayar da shugaba mai-ci John Dramani
Mahama a zaben da aka gudanar a watan jiya.
Shugabannin kasashen Afrika 11 ne ake sa ran
za su halarci bikin ranstuwar, wanda zai gudana
a dandalin Independence Square da ke birnin na
Accra.
Bukin rantsarda sabon shugaban Ghana ya kankama Bukin rantsarda sabon shugaban Ghana ya kankama Reviewed by Mr Amanagurus on January 06, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.