A cikin yukurin su na dakile yada labaran karya marasa tushe, kamfanin zumunta na yanar gizo Facebook, sun rufe shafufukan mutane sama da dubu 30,000 a kasar France.
Kamfanin mai mazauni a karamar hukumar Silicon Valley, dake jihar Califonia ta Amurka, suna kokarin ganin sun taimaka wajen ganin an yaki wannan matsalar, duk dai da cewar gwamnatocin kasashen turai na adawa da yunkurin kamfanin.
Mafi akasarin manyan kamfanonin yanar gizo, kamar su Twitter, YouTube, da facebook, suna fuskantar matsanancin bincike a yankin kasashen Turai, don ganin ba’ayi amfani da shafufukan su wajen yada ta’addanci a duniya.
A ‘yan watanni masu zuwa ne, za’a gabatar da zabe a kasashen France da Germany, don haka ana gargadin kamfanonin da su kokarta wajen ganin basu bada wata dama ba, wajen aika sakonnin da basu da asali.
Su bada tasu gudun mawa, wajen ganin ba’a yada duk wani labari da bashi da tushe ba, koda kuwa ya kankantar shi yake, haka duk wani shafi da bashi da kwararan bayanai, to su tabbatar sun kulle shi.
© Dandalinvoa.
NEWS: KAMFANIN FACEBOOK SUN KULLE SHAFUKAN MUTANE 30,000
Reviewed by Mr Amanagurus
on
April 19, 2017
Rating:
No comments: