Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya shirya don komawa gida Nijeriya bayan tabbatar da samun lafiya da ya yi a zaman jinyarsa a Birtaniya.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa a wannan Asabar, ta ce abin kawai da ya ragewa shugaban shi ne amincewar likitocinsa wadanda sai da izininsu ne Buharin ya ce zai dawo gida.
‘Yan Najeriyar da dama dai na kokwanton ko shugaban mai shekaru 74 na da karfi da lafiyar jagorantar kasar. Ko a ‘yan kwanakin na ma dai an gudanar da zanga-zangar neman ko ya koma aiki, ko kuma ya yi murabus saboda halin lafiyar ta sa. A bana dai kwanakin da shugaba Buhari ya yi a Birtaniya sun zarta wadanda ya yi a Nijeriyar.
A Shirye Nake Na Dawo Nijeriya Domin Ci Gaba Da Aiki, Cewar Shugaba Buhari
Reviewed by Mr Amanagurus
on
August 12, 2017
Rating:
No comments: