Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

An Kama Dattijon Da Ya Yiwa Yaro Dan Shekara 9 Fyade Ya Kashe Shi Har Lahiri

‘Yan sanda sun kama wasu dattawa 2 a jihar Kebbi wadanda ke wa kananan yara maza fyade.
An gabatar da wadanda ake zargi ga ‘yan jarida a hedikwatar ‘yan sanda da ke Birnin Kebbi a jiya Lahadi 20 ga watan Agusta, 2017
Kwamihshinan ‘yan sanda na jahar, Ibrahim Kabiru, bayan ya gabatar da wadannan mutanin a gaban ‘yan jarida ya bayyana cewa wanda ake zargi mai suna Malam Ibrahim Yohana Mudi ya yiwa yara maza biyu ‘yan shekara 10 da 12 fyade daga kananan hukumomin Kalgo da Zuru.
Shi kuma Dantani Sani mai shekaru 45 a Duniya daga garin Zauro ya yiwa wani dan shekara 9 fyade wanda ta sanadiyyar yin fyade yaron ya mutu.
“An kama Sani daga yankin Sabon Gari a karamar hukumar Zauro akan labarin da aka samu na yiwa wani yaro mai suna Ibrahim Muhammadu Dangi fyade dan shekara 9, wanda yanzu haka ya rasa ransa ta sanadiyyar hakan.
Shi wannan mutumin ya aika laifin ne a 31 ga watan Yuli, 2017. A nan take bada dadewa ba yaron da aka yiwa fyade ya kama zawo da gudawa, bayan wasu ‘yan awanni kadan sai ya cika a ranar da abun ya faru.” Kwamishinan ya ce.
Kwamishinan a karkashe ya ca za a gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu nan bada dadewa ba.
An Kama Dattijon Da Ya Yiwa Yaro Dan Shekara 9 Fyade Ya Kashe Shi Har Lahiri An Kama Dattijon Da Ya Yiwa Yaro Dan Shekara 9 Fyade Ya Kashe Shi Har Lahiri Reviewed by Mr Amanagurus on August 21, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.