Daga IBRAHIM SHEME
Allah mai zamani; a bana ma ba a samu wasu wakokin gargajiya na Hausa da su ka yi fice kamar na zamani da ake bugawa da fiyano ba.
Masu son Mamman Shata da Musa Dankwairo da sauran mawakanmu na gargajiya sun ci gaba da sauraren mawakan saboda sabo da kuma rike al'ada, to amma wakokin da aka fi saye ko aka fi saurare a kafafen yada bayanai da su ka hada da rediyo, talbijin da soshiyal midiya su ne wakokin da matasa ke yi da kayan kida na zamani.
Bayan bincike mai zurfi, mun zakulo wakokin Hausa guda 10 da jama'a su ka fi saurare a wannan shekarar ta 2017, daga cikin dimbin wakoki na mawaka daban-daban.
Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.
1. UMAR M. SHARIFF (tare da Murja Baba) - "Jirgin So" (daga fim din 'Mansoor')
Wakar "Jirgin So" fito ne a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu. Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da fitacciyar zabiya Murja Baba.
Haka kuma 'Mansoor' shi ne fim na farko da Umar ya fito a ciki a matsayin dan wasa. Hasali ma dai shi ne jarumin fim din, inda ya fito tare da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahya a matsayin jarumar shirin.
Wakar 'Mansoor' ta yadu ne a dalilin ficen Ali Nuhu a industiri din fina-finan Hausa, da kuma kasancewar Umar M. Shariff daya daga cikin mawakan da su ka fi yin tashe a wannan lokaci.
"Jirgin So" wakar soyayya ce tsakanin saurayi da budurwa. A cikinta, gwanayen mawakan (Umar M. Shariff da Murja Baba) sun nuna kwarewa wajen karya murya da kuma zuba kalmomi na shauki.
An yi ittafaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana. An yada ta sosai a kafofin sada zumunta na zamani a yunkurin tallata fim din. Hakan ya sa lokacin da fim din ya fito, matasa sun yi caa zuwa gidajen sinima domin su kalli yadda aka yi rawar wakar.
2. SADIQ ZAZZABI (tare da Maryam Fantimoti) - "Maza Bayan Ka"
Jigon wakar "Maza Bayan Ka" ta Sadiq Zazzabi dai shi ne zambo, ba kambawa ba kamar yadda wasu ke zato.
Duk da yake mawakin bai ambaci wanda ya ke yi wa zambon ba, masu lura da siyasar jihar Kano sun san takaddamar da ake yi tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da masu adawa da shi, musamman a jihar inda ya yi gwamna kafin zuwan sa Majalisar Tarayya.
Wakar na kunshe ne da kalamai na muzanta babban abokin adawar Kwankwaso.
Wani al'amari da ya sa wakar ta kara yin fice shi ne kama Sadiq Zazzabi tare da gurfanar da shi a gaban kotu da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi a bisa zargin ya saki wakar kafin hukumar ta ba shi takardar izinin fitar da ita.
3. ABDUL D. ONE (tare da Khairat Abdullah) - "Abin Da Ke Cikin Rai Na" (daga fim ]in 'Mansoor')
Wannan wakar ita ce 'yar'uwar wakar "Jirgin So" ta Umar M. Shariff; dukkan su sun fito a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu.
Wakar soyayya ce. Abdul D. One, daya daga cikin yaran Umar M. Shariff, shi ne ya rera ta tare da mawakiya Khairat Abdullah. Wannan waka dai ta fito daga Kaduna, akasin yawancin wakokin zamani da ke fitowa daga Kano.
Abin da ya kara daga wakar shi ne kasancewar ta cikin fim din Ali Nuhu mai suna 'Mansoor' wanda ya na daga cikin manyan finafinan shekarar 2017.
Wannan fim ya sha talla a shafukan sada zumunta, da yake Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, shi ne ya shirya fim din kuma ya ba da umarni, sannan jarumin shirin, wato Umar M. Shariff, mawaki ne mai dimbin masoya, wadanda ke so su ga yadda ya yi a fim din.
Masoyan Ali da na jaruman fim din sun taimaka wajen tallata wakar a Instagram ta hanyar yada bidiyon ta da kuma shirya nasu bidiyon na rawar wakar.
4. DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA) - "Buhari Ya Dawo"
Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya fitar da wannan wakar ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga London, inda ya shafe watanni yana jinya.
Sanin kowa ne an yi ta shaci-fadi kan rashin lafiyar, saboda haka 'yan Nijeriya da dama sun zaku su ga dawowar sa.
Don haka sakin wakar a daidai lokacin na da wuya sai ta karbu a wajen masu saurare.
Rarara ya yi waar ne a matsayin martani ga masu adawa da Buhari, musamman masu cewa rashin lafiyar zai hana shi ci gaba da mulki. Da ma can Rarara magoyin bayan Shugaba Buhari ne.
5. UMAR M. SHARIFF (tare da Khairat Abdullah) - "Rariya" (daga fim din 'Rariya')
Umar M. Shariff ya ci gaba da rike kambin sa na kasancewa daya daga cikin manyan mawakan wannan zamanin da wakar "Rariya" wadda ta fito a cikin fim din 'Rariya'. Shi da Khairat Abdullah suka rera wakar.
Jigon wakar shi ne soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cewar saurayin, ya yi tankade da rairaya na soyayya da rariya ne, a karshe ya yi dacen samun budurwar tasa a matsayin "tsabar" da wannan tankaden ya samar.
Ya ce: "Tankade na yo na sa rariya, Ke ce ki ka zam tsaba, Zabi na a soyayya." Ita ma ta mayar masa da wadannan kalmomin, tare da nuna masa cewa za ta yi masa sakayya da ba shi zuciyar ta.
Kalmomin soyayya da ake furtawa a wa}ar sun taba zukatan matasa matuka.
To amma ficen wakar ya samo asali ne daga kansancewar ta wakar da ta jagoranci fim din Rahama Sadau, fitacciyar jarumar da sunan ta ya kara yaduwa saboda korar ta daga Kannywood da kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta yi a shekarar da ta gabata.
Da yake 'Rariya' shi ne babban fim din da Rahama ta shirya a bana, masoyan jarumar sun yi mata kara wajen tallata wakar a shafukan su na Instagram.
Kwatankwacin dai yadda su ka yi wa wakokin fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu, sun rika shirya bidiyo na rawar waka nasu na kan su, su na turawa.
Babu mamaki, lokacin da za a nuna fim din a gidajen sinima, matasa sun rika yin tururuwa zuwa wajen kallo, don su ga yadda aka yi rawar wakar.
6. ADO ISA GWANJA - "Ayyaraye Indosa, A Sha Ruwa"
An fi sanin Ado Isa Gwanja ne da wakar "Kujerar Tsakar Gida" wadda ta kasance waka mafi karbuwa ga matan biki a fadin arewacin Najeriya tun bayan da ya rera ta shekara biyu kenan.
Ba a daina jin "Kujerar Tsakar Gida" ba, sai kuma Gwanja ya so ya rike kambinsa na jagaba a wakokin gidan biki da wakar "Mata Mu kame kam".
To amma wakar da ta fi jan hankali a bana ita ce wakarsa mai taken "Indosa".
Akasin sauran, ita ba wakar rawar cashewa ko girgiza jiki ba ce; waka ce ta saurare wadda kuma za a iya rausayawa.
A cikin ta, Gwanja na yabon kan sa ne saboda ficen da ya yi a matsayin mawakin gidan biki. Ya yi nuni da cewa yanzu ya zama gamji a cikin mawaka, wato ya gagara a sare shi.
Ya ce duk da yake wasu na cewa mata ya ke yi wa waka, to ya tabbatar in har ya doka wakar sa, har mazan ma sai sun taka.
7. NURA M. INUWA - "Ranar Aure Na"
Nura M. Inuwa ya rera wakar "Ranar Aure Na" ne sakamakon auren da ya yi a wannan shekarar a Jihar Katsina.
A wakar, ya yi godiya ga Allah da ya nuna masa ranar aurensa da kuma jama'ar da su ka je bikin auren, tare da bayyana farin ciki da wannan al'amari.
Haka kuma ya tabo masu adawa da shi a kan wannan aure, ya nuna cewa Allah ya yi ko da su ba su so. Ita ma amaryar, ya yi addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya.
Da yake Nura mawaki ne mai dimbin masoya saboda wakokinsa na soyayya, kuma an jima ana jiran ranar aurensa, wakar ta karbu sosai, musamman wajen matasa.
8. ASMA'U SADIQ - "Dolin-Dolin"
Asma'u Sadiq ta zama kallabi a tsakanin rawunna da wakarta ta "Dolin-Dolin". Waka ce ta gada. Jigon wakar shi ne soyayyar samari da 'yanmata, musamman a gargajiyance.
Wakar ta yi fice musamman saboda yawan saka ta da ake yi gidajen rediyo na FM a garuruwan Arewa.
Duk da yake an kira ta "Dolin-Dolin", wannan waka ba amshi daya ba ne ta ke da shi; hade-hade ce ta wasu wakokin gada guda biyar, wato "Dolin-Dolin", "Soriyalle Maigida Na", "Kacalle-Kacalle Mu Yi Gada", "Mai Zamani 'Yanmata", da "Warai-Warai".
A karshen wakar, zabiyar ta kawo wani baiti da ya yi kama da na wakokin hip-hop.
9. MORELL - "Aure"
Wakar "Aure" ta Morell ce kan gaba a bana cikin rukunin wakokin hip-hop. Duk da yake tun bara ya saki wakar, amma dai ba a samu wadda ta doke ta a fagen ba.
Wakar ta rike matsayin ta ne bayan fitar bidiyo ]in ta da ya faru a cikin wannan shekara ta 2017, wanda Moe Musa ya ba da umarni. Akwai Ali Nuhu a bidiyon.
Sunan Morell na asali dai shi ne Musa Jikan Musa, kuma ya yi wasu wakokin wadanda su ka hada da "Karota", "Borno", "Safay", "Ganga Da Garaya" da kuma "Ba Wani Bugatti".
Wakokin hip-hop na Hausa da su ka kara da wannan wakar sun hada da wadda marigayi Lil Ameer ya yi mai taken "Dance for Me - Ni Ameer Na Kowa Ne" da wakar "Arab Money" ta Nomiis Gee.
10. NAZIRU M. AHMAD - "Rawa, Rawa"
Naziru M. Ahmad ya yi fice wajen wa}o}in sarakuna da kidan gargajiya, musamman wajen yin amfani da tambura da tallaye da ganguna da algaitai.
Amma ya kan yi wakoki na soyayya ko na aure, da sauran su.
A bana, hazikin wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka, ya rike mukamin sa ta hanyar sakin wakar "Rawa, Rawa".
Wakar biki ce wadda ya yi hikimar kawo ta da salon gargajiya, ana buga ganguna, sannan ga 'yan amshi su ma su na sako kalmomi kwakwankwacin yadda su Musa Dankwairo k

Wakokin Hausa da suka fi shahara a shekarar 2017
Reviewed by Mr Amanagurus
on
December 30, 2017
Rating:
No comments: