Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

An tsare mai shirya fina-finai saboda zargin sace wayoyin hannu

Wata kotu a jihar Legas ta bayar da umarnin a ci
gaba da tsare fitatcen mai shirya fina-finai
Yarabanci, Seun Egbede, bayan da aka zarge shi
da satar wayoyin hannu kirar iPhone guda goma.
Sai dai kuma Egbegbe - wanda ya yi hadakar aiki
tare da jarumar fim Toyin Aimakhu - ya karyata
zargin.
Masu shigar da kara sun zarge shi da arcewa da
gudu daga kantin da ya kwashe wayoyin ya
kuma fada cikin wata mota da ke a jiransa, a
lokacin da mai wurin yake lissafa kudin wayoyin.
An dai kama shi daga baya, inda aka lakada
masa duka, kafin jami'an tsaro suyi awon gaba
da shi, in ji jaridar Vanguard.
An samu hatsaniya a cikin kotun da ke Ikeja,
bayan da magoya bayan mai shirya fim din suka
yi barazanar daukar mataki kan duk wanda ya
dauki hotonsa.
An tsare mai shirya fina-finai saboda zargin sace wayoyin hannu An tsare mai shirya fina-finai saboda zargin sace wayoyin hannu Reviewed by Mr Amanagurus on November 25, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.