Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Griezmann ba zai buga karawa da Real ba

Watakila dan wasan Atletico Madrid, Antoine
Griezmann, ba zai buga karawar da kungiyar za
ta yi da Real Madrid a ranar Asabar, sakamakon
raunin da ya yi.
Griezmann ya yi rauni ne a fafatawar da Faransa
ta ci Sweden 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin
duniya da suka yi a ranar Juma'a.
Tuni dan kwallon ya koma Spaniya domin yin
magani, kuma hakan na nufin ba zai buga wasan
sada zumunta da Faransa za ta yi da Ivory Coast
ba a ranar Talata.
Atletico ce za ta karbi bakuncin Real Madrid a
wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga
wasannin mako na 12 a ranar Asabar.
Griezmann mai shekara 25, shi ne dan wasan
Atletico da ya fi yawan ci wa kungiyar kwallaye a
kakar bana, inda ya ci guda shida.
Griezmann ba zai buga karawa da Real ba Griezmann ba zai buga karawa da Real ba Reviewed by Mr Amanagurus on November 14, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.