Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ivory Coast
Laurent Pokou, wanda ake wa kallon wani kusa
a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka, ya rasu,
yana da shekara 69.
Laurent Pokou ya taka leda daga shekarun 1960
zuwa 1970 a kungiyar ASEC Mimosas inda ya
fara kwallonsa.
Ya buga wa kasarsa kwallo sau 70.
Pokou ya kuma buga kwallo a kulob din Nancy na
Faransa daga 1977 zuwa 1978, inda ya yi wasa
tare da Michel Platini.
Ana tuna shi saboda tarihin da ya kafa na zura
kwallaye mafiya yawa - 14 - da wani dan kwallo
tilo ya yi a gasar cin kofin kasashen Afirka.
Sai bayan shekara 30 sannan dan wasan Kamaru
Samuel Eto'o ya shafe wannan tarihi a shekara
ta 2008 a gasar da aka yi a Ghana.
Pokou ya mutu ne a birnin Abidjan bayan ya sha
fama da rashin lafiya.
Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu Reviewed by Mr Amanagurus on November 14, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.