Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa

An tsaurara matakan tsaro a manyan biranen
duniya yayin da ake shirin shiga sabuwar
shekara ta 2017.
A wasu biranen kasashen yamma, da suka hada
da London, da Brussels da Berlin, an girke karin
dubban 'yan sanda gabanin bukukuwan shiga
sabuwar shekarar.
An sanya shingaye na kankare a wuraren taruwar
jama'a a tsakiyar birnin Paris, da Madrid da New
York don kare aukuwar hare-hare da manyan
motoci, kwatan-kwacin wadanda aka kai a baya a
biranen Berlin da Nice.
An hana jama'a yin shagulgulan sabuwar
shekarar a Dhaka, babban birnin Bangladesh,
wanda ya yi fama da hare-haren 'yan bindiga
masu alakanta kansu da Musulunci.
An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa Reviewed by Mr Amanagurus on December 31, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.