Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Ni ma zan iya amfani da karfi kan ECOWAS — Jammeh

Shugaban Gambia mai barin gado, Yahaya
Jammeh, ya ce, idan tura ta kai bango zai iya
yakar Kungiyar Habaka Tattalin arzikin Afirka ta
Yamma, ECOWAS ko kuma CEDEAO.
A wani sakon taya murnar sabuwar shekara ga
'yan kasar, da aka yada a kafar sada zumunta ta
Youtube, Jammeh, ya ce, kungiyar na wuce gona
da iri a Gambia.
Ya ce ECOWAS na nuna banbanci tsakaninsa da
Adama Barrow.
Saboda haka ne ya nemi kungiyar da ta san inda
dare ya yi mata domin a cewarsa bata da
hurumin yin katsalanda a kasar.
Yahya Jammeh dai ya ce shi ne mutumin da ya
lashe zaben kasar na farkon watan Disambar
2016, bayan da da fari ya amince da shan kaye.
Kungiyar ECOWAS dai a taron da ta yi a Abuja,
babban birnin Najeriya, ta ce, za ta iya amfani
da karfi wajen tunbuke Yahya Jammeh.
Ni ma zan iya amfani da karfi kan ECOWAS — Jammeh Ni ma zan iya amfani da karfi kan ECOWAS — Jammeh Reviewed by Mr Amanagurus on December 31, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.