Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Zakaran Formula 1 na duniya Rosberg ya yi ritaya

Zakaran tseren motocin Formula 1 na duniya
Nico Rosberg ya sanar da cewa ya yi ritaya nan
take.
Dan tseren dan kasar Jamus mai shekara 31 ya
ci babbar gasarsa ta farko ranar Lahadi, bayan
ya doke Lewis Hamilton.
Rosberg ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa
"Na kai kololuwar ganiyata don haka wannan
matakin da na dauka shi ne ya dace."
Rosberg ya lashe manyan gasar tseren motoci
tara cikin 21 da aka yi a bana, inda ya doke
Hamilton wanda sau uku yana zama zakaran
tseren.
Ya kara da cewa,"A shekara 25 da na yi ina yin
tseren motoci, babban burina shi ne na zama
zakaran Formula 1 na duniya."
Zakaran Formula 1 na duniya Rosberg ya yi ritaya Zakaran Formula 1 na duniya Rosberg ya yi ritaya Reviewed by Mr Amanagurus on December 02, 2016 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.