Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Albishiri Ga Masu Sha Awar Fitowa a Fim Din Hausa Ga Dama Tasamu (Karanta)

Ko Kuna Da Labarin Sabon Shirin “GISHIRIN RAYUWA”?
A karon farko farfajiyar shirya finafinan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood za su dibi mutanen gari dake da sha’awar fitowa a fim cikin sabon shirin wasan kwaikwayo da za’a fara dauka kwanan nan.
Shirin mai suna “GISHIRIN RAYUWA” zai maida hankali ne fannin ilimantarwa da nishadantarwa da fadakarwa, kuma zai bambanta da yadda aka saba shirya sauran fina-finai.
Yanzu haka dai an bude kofa ga duk mai sha’awar shiga ko fitowa a cikin sabon shirin wasan kwaikwayon. Duk mai sha’awa zai je kai tsaye ayi masa gwaji domin tantancewa kamar haka:-
A Jihar Kano
Za’a yi taron tantance yan wasan ne:-
A Ranar Asabar da Lahadi, 22 da 23/07/2017
Waje: Dankin Taro Na Mumbayya House dake Gwammaja Kano.
Lokaci: Da Karfe 9:00 na safe
Domin karin bayani sai a tuntubi lambar waya 0703 883 8890
A JOS
Za’a yi taron tantance yan wasan ne kamar haka:-
A ranar Asabar da Lahadi 29 da 30/07/2017
Waje: Mega Park dake kan titin Bauchi, Bauchi ring road, Jos
Lokaci: Da karfe 9:00 na safe
Marubutan shirin (Writers)
Nazir Adam Salihi
Nasir Nid
Nazir Alkanawi
Shiryawa (Producer)
Ahmed Muhammed Sarari
Mai bada umurni (Director)
Falalu Dorayi
Kamfanin SKM tare da hadin guiwar Kannywood Entertainment ne suka dauki nauyin shirin.
Domin karin bayani sai a tuntubi: Lambar waya 07038838890
Zamu cigaba da kawo maku rahoton yadda ta kaya a wajen tantancewar. Allah yaba mai rabo sa’a
Albishiri Ga Masu Sha Awar Fitowa a Fim Din Hausa Ga Dama Tasamu (Karanta) Albishiri Ga Masu Sha Awar Fitowa a Fim Din Hausa Ga Dama Tasamu (Karanta) Reviewed by Mr Amanagurus on July 22, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.