Music

banner image

Custom Widget

3/Business/post-per-tag

Toh Fa! Za’a Shirya Fim ɗin Shekau A Masana’antar Kannywood (HOTO)

Shahararren kamfanin shirya fina finai na Kannywood, UK Entertainment ya kammala tsaf don shirya wani kasaitaccen fim mai suna Aliko, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Majiyar amanagurus.com.ng ta ruwaito cewar wannan sabon fim da ake shirin yin sa, zai kun shi kwaikwayon ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ne, wanda Nasir Gwangwazo ya rubuta labarin.
Duk a cikin shirin, za’a kwaikwayi shugaban kungiyar ta’addancin, wato Abubakar Shekau, inda aka sanya shahararren jarumi Sadiq Sani Sadiq a matsayin wanda zai fito a matsayin shugaban Boko Haram, Shekau.
Bugu da kari wannan Fim ya samu bada umarni daga Yaseen Auwal, yayin da Umar UK ne ya shirya shi, sai Nasir Gwangwazo wanda ya tsara shi.
Toh Fa! Za’a Shirya Fim ɗin Shekau A Masana’antar Kannywood (HOTO) Toh Fa! Za’a Shirya Fim ɗin Shekau A Masana’antar Kannywood (HOTO) Reviewed by Mr Amanagurus on July 22, 2017 Rating: 5

No comments:

Powered by Blogger.